'Yan Liverpool Agger da Johnson sun ji rauni

agger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daniel Agger da Glen Johnson.

Liverpool ta fuskanci koma baya sakamakon raunin 'yan kwallonta na baya Daniel Agger da Glen Johnson.

Agger ya jimu ne a wasansu da West Brom kuma ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda turgude gwiwa.

A yayinda shi kuma Johnson zai yi jinya ta wata guda saboda rauni a kafadarshi.

Sai dai Fabio Aurelio ya komo horo bayan doguwar jinya.

A halin da ake ciki a yanzu kocin Liverpool Kenny Dalglish duk da wannan matsalar ya soma murnar dawowar Jonjo Shelvey wanda aka yiwa tiyata a watan Fabarairu.

Sai dai raunin Agger da Johnson ya janye Liverpool zata yi karancin 'yan kwallon baya har zuwa karshen kakar wasa ta bana.