Zamu nemi zira kwallo a Stamford Bridge-Ferguson

fergie
Image caption Karo da karo sai rago

Sir Alex Ferguson yace Manchester United zata tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai idan har suka ci kwallo a bugun farko tsakaninsu da Chelsea.

Kocin United zai maida hankali don gannin 'yan wasanshi sun zira kwallo a Stamford Bridge don basu dama idan har aka zo buga wasan bugu na biyu.

Ferguson yace"idan muka koma Old Trafford zamu fisu dama, don da wuya su doke mu".

Ferguson ya kara da cewar"a wannan lokacin ina farin cikin ganin cewar wasan bugu na biyun a Old trafford ne".

United zata fuskanci wasan ne a Old Trafford a dai dai lokacin da ta shafe shekaru tara bata samu nasara ba a Chelsea

Kyaftin din United Nemanja Vidic ya nuna fargabarshi akan yadda Chelsea ke kokarin yin ramuwar gayya.

Shi kuma Frank Lampard na Chelsea na tsoron Wayne Rooney.