Kanoute zai shafe makwanni uku yana jinya

Frederic Kanoute Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Frederic Kanoute

Dan kwallon Mali wanda ke taka leda a Sevilla Frederic Kanoute zai shafe makwanni uku yana jinya saboda raunata kafarshi ta dama.

Kanoute ya jimu ne a wasan da suka doke Real Zaragoza daci uku da daya a Lahadi.

Kawo yanzu dai dan wasan ya zira kwallaye tara a gasar La Liga a kakar wasa ta bana.

Sevilla a halin yanzu itace ta shida akan teburin gasar La Liga, abinda zai sa ta iya tsallakewa zuwa gasar Europa a kakar wasa mai zuwa.

Amma duk da haka Barcelona ta dara Sevilla da maki 36.