Alkalin wasa ne ya cutar damu-Ancelotti

ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti na tuhumar alkalin wasa bayan Chelsea ta sha kashi daci daya me ban haushi a hannun Manchester United a bugun farko na zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun Turai.

Ancelotti yace "azihiri yake Patrice Evra ya kada Ramires amma sai alkalin wasa Undiano Mallenco yaki baiwa mai daukar bakunci damar farke kwallon da Wayne Rooney ya zira".

Ramires na tafiya da kwallo sai Evra yasa kafa ya tadiye shi sai dan kwallon ya fadi a gabda ragar United.

Amma sai alkalin wasan wanda dan kasar Spain ne yaki bada bugun fenariti daga bisani sai Ancelotti ya kalubalanci alkalin wasan bayan an tashi wasan.

Abinda hakan ke nufi shine dole sai Chelsea ta zage damtse a bugu na biyu da zasu yi a Old Trafford a ranar 12 ga watan Afrilu.