An ci tarar Zenit saboda wulakanta Carlos

carlos Hakkin mallakar hoto
Image caption An nunawa Carlos bawon ayaba

Hukumar dake kula da kwallon Rasha ta ci tarar kungiyar Zenit St Petersburg tarar dala dubu goma bayan wani mai goyon bayanta ya baiwa Roberto Carlos ayaba.

Lamarin ya auku ne a watan Maris kafin kungiyar Zenit ta kara da kungiyarsu Carlos din wato Anzhi Makhachkala.

Bayan 'yan kwanaki sai Zenit ta sanarda cewar ta haramtawa mutumin shiga filinta na muddin rai.

A shekara ta 2008 an ci tarar Zenit dala dubu hamsin da takwas bayan magoya bayanta sun wurga bawon ayaba suna ta kiran bakaken 'yan kwallon Marsielle birai.

Carlos mai shekaru 37 yana cikin tawagar 'yan kwallon Brazil da suka je gasar cin kofin duniya har uku.

Ya koma Anzhi Makhachkala a bana daga kungiyar Corinthians ta Brazil.

An yawan nuna wariyar launin fata a Rasha wacce zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018.

Zenit ta kasance kungiya daya tal da bata taba kulla yarjejeniya da wani dan asalin Afrika ba.