Gerrard ba zai kara taka leda ba a kakar bana

Steven Gerrard
Image caption Steven Gerrard ya dade yana fama da rauni

Dan wasan Liverpool Steven Gerrard ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana, sakamakon raunin da yake fama da shi. Dan wasan na Ingila ya komo horo ne a makon da ya gabata bayan tiyatar da aka yi masa a watan Maris, amma sai ya kara samun makamancin raunin a ranar Juma'a. Dan wasan mai shekaru 30 ya shafe mako guda ana yin nazari a kansa, abinda yasa koci Kenny Dalglish ya tabbatar da wannan labarin a lokacin da 'yan wasan ke atisayi. "Ba mu san zahiri ko menene matsalar ba," a cewar Dalglish.

"Za mu jira mu ji daga likitocin da zai gani, amma dai ba zai kara taka leda a kakar bana ba."