Kwesi ya maye gurbin Amos Adamu a WAFU

kwesi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwesi Nyantakyi

Hukumar dake kula da kwallon kafa a yammacin Afrika wato WAFU ta zabi Kwesi Nyantakyi na Ghana a matsayin shugabanta na riko.

A ranar Asabar ne a Banjul, WAFU ta dakatar da shugabanninta da kuma nada shugabannin riko.

An kira taron ne don neman wanda zai maye gurbin shugaban WAFU Amos Adamu wanda aka dakatar.

Fifa ce ta dakatar da Adamu na shekaru uku saboda kokarin karbar cin hanci wajen zaben kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.

Amma dai hukumar CAF ta ki amince da sabon zabe a WAFU don maye gurbin Adamu.

Sai a ranar 31 ga watan Mayu WAFU zata tattauna a Zurich akan batun sabon zaben.

Sauran 'yan kwamitin riko sune Augustin Senghore na Senegal da Jose Lobato da Guinea Bissau da kuma dan Gambia Seedy Kinteh.

Sauran kuwa sune Idris Diallo na Ivory Coast, da Theodore Sawadogo na Burkina Faso sai kuma dan Mali Hamadou Cisse.

Haka zalika, WAFU na tunanin dauke shalkwatarta daga Ivory Coast tashin hankali a kasar.

Mohammed Bin Hammam dan Qatar wanda ke takarar shugabancin Fifa a wata mai zuwa, ya halarci Banjul don neman kuri'ar 'yan Afrika.