Bayern Munich ta sallami Louis van Gaal

van  gaal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Loius van Gaal

Bayern Munich ta sallami kocin 'yan kwallonta Louis van Gaal ba tare da jinkiri ba.

Dan shekaru hamsin da tara, tsohon kocin Barcelona dama dai a karshen kakar wasa ta bana ya kamata ya tafi.

Bayern a yanzu itace ta hudu Bundesliga kuma tana tangal tangal a kokarin neman gurgin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai a badi.

A halin yanzu mataimakin Van Gaal Andries Jonker shine zai cigaba da jagorantar kulob din zuwa karshen kakar wasa ta bana kafin Jupp Heynckes ya koma.

A kakar wasan data wuce Van Gaal ya jagoranci Bayern ta lashe gasar Jamus sannan ta buga wasan karshe na gasar zakarun Turai, inda Inter Milan ta doke su daci biyu da nema a birnin Madrid.