Kroenke ya kara hannun jarinsa a Arsenal

Stan Kroenke
Image caption Stan Kroenke

Dan kasuwa a Amurka Stan Kroenke ya kara kason hannun jarinsa a Arsenal inda ya koma fiye da kashi sittin da biyu cikin dari, kuma ya amince ya karbe jarin kulob din baki daya.

Kokarin mallakar daukacin kulob din ya taso ne bayan kamfanin Kroenke Sports Enterprises ya sayi hannun jarin Danny Fiszman na kashi 16.1 cikin dari da kuma na Lady Nina Bracewell-Smith wato kashi 15.9 cikin dari.

Kronke a shekara ta 2007 ne ya sayi hannun jari a Arsenal a karon farko inda ya sayi kashi 9.9 cikin dari.

Kronke ya ce "mun yi murnar samun karin dama don cigaba da saka kanmu wajen ciyyar da Arsenal gaba.

Ya kara da cewar"Arsenal kungiya ce ta musaman mai tarihi da al'ada kuma tana da kocin wanda ya kware wato Arsene Wenger.

Kulob Kulob na Ingila wadanda 'yan kasashen ketare suka malaka:

*ASTON VILLA - Randy Lerner *BIRMINGHAM - Carson Yeung *BLACKBURN - Venky's *CHELSEA - Roman Abramovich *FULHAM - Mohamed Al Fayed *LIVERPOOL - Fenway Sports *MAN CITY - Abu Dhabi United *MAN UTD - Glazer family *SUNDERLAND - Ellis Short