An nada Oblias mataimakin kocin Super Falcons

Oblias Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thomas Oblias

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Najeriya-NFF ta tabbatarda daukar hayar dan Jamus Thomas Oblias a matsayin mataimakin kocin Super Falcons.

Obliers mai shekaru 43 zai yi aiki tare da Eucharia Uche wacce itace babbar koci.

Ya amince da yarjejeniyar wattani hudu tare da Najeriya daga watan Afrilu.

Kakakin Nff Ademola Olajire ya bayyana cewar dan Jamus din nada kwarewa akan harkar kwallon mata.

Najeriya ta tsallake zuwa gasar cin kofin mata ta duniya tunda aka fara gasar a shekarar 1991.

Super Falcons na rukuni mai sarkakiya tare da Jamus da Faransa da kuma Canada.

Kasashe goma sha shida ne zasu fafata a gasar cin kofin duniya daga ranar 26 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli a Jamus.