Sakaci nane yasa Liverpool ta doke mu-Mancini

mancini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya amsa laifin cewar sakacinshi ne ya janyo suka sha kashi a wajen Liverpool daci uku da nema.

Andy Carroll ne ya zira kwallaye biyu a yayinda Dirk Kyut yaci guda a wasan, inda Liverpool ta fara tunanin samun gurbin zuwa gasar Europa.

Mancini yace "bamu buga komai ba a mintuna 20 na farko lokacin da Liverpool ta haskaka, laifi na ne".

Mancini dai yayi canjin 'yan wasa uku a tawagar da City ta lallasa Sunderland daci biyar da nema.

A halin yanzu City na cikin rudu, a yayinda take shirin fafatawa da Manchester United a gasar cin kofin FA. result all round."