FIFA:Har yanzu Ghana ce ta farko a Afrika

fifa Hakkin mallakar hoto
Image caption FIFA

Bisa jerin yadda karfin kasashen yake a fagen kwallon kafa a watan Afrilu, hukumar dake kula da kwallon duniya Fifa ta bayyana kasar Ghana a matsayin ta farko a nahiyar Afrika amma kuma itace ta goma sha biyar a duniya.

Ivory Coast a yanzu itace ta biyu a Afrika amma ta ashirin da daya a duniya a yayinda Masar take ta uku a Afrika ta talatin da shida a duniya.

Najeriya ta koma talatin da takwas a duniya amma ta hudu a Afrika sai Afrika ta Kudu ta biyar amma ta talatin da tara a duniya.

Jerin kasashen Afrika:

1. Ghana 2. Ivory Coast 3. Masar 4. Najeriya 5. Afrika ta Kudu 6. Algeria 7. Burkina Faso 8. Cameroon 9. Senegal 10.Libya

Jerin kasashe goma na farko a duniya:

1. Spain 2. Netherlands 3. Brazil 4. Germany 5. Argentina 6. England 7. Uruguay 8. Portugal 9. Italy 0. Croatia