Torres zai haskaka nan gaba kadan-Ferguson

Fernando Torres Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu Torres bai zira kwallo a Chelsea ba

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce a kara hakuri da dan wasan Chelsea Fernando Torres domin zai fara haskakawa nan gaba kadan.

Dan wasan wanda aka saya fan miliyan 50, har yanzu bai zira kwallo ba tun bayan zuwansa Chelsea, kuma an cire shi bayan an dawo rabin lokaci a wasan da United ta doke su da ci 2-1.

"Ban ga dalilin a jiye shi ba, bayan an kashe makudan kudade an saye shi," a cewar Ferguson.

"Ba ya kokari a yanzu, amma matashi ne, kuma yana da shekaru nan gaba".

Ferguson ya kara da cewa Chelsea sun yi nasara wajen sayen Torres, kuma babu wata kungiya da ba ta son dan gaba mai kyau kamarsa.

An dai ta cece-kuce kan matakin kocin Chelsea Carlo Ancelotti na fara wasan da Torres maimakon Didier Drogba.