Ba zan sayarda hannun jari na ba a Arsenal-Usmanov

usmanov
Image caption Alisher Usmanov

Attajirin dan kasuwa Alisher Usmanov ya ce ba zai sayarwa da Stan Kroenke nasa bangaren hannun jarinsa ba na kungiyar Arsenal.

A farkon wannan makon ne Kroenke ya kara yawan hannun jarinsa ya koma kashi 63 cikin dari, abinda yasa ya nema saye sauran hannayen jarin jama'a a kulob din.

Amma Usmanov wanda keda jarin kashi 27 cikin dari na kulob din yace"ba zan sayarda na hannun jari na ba".

Ya kara da cewar"ina son Arsenal shi yasa na keda hannun jari a kulob".

Dan kasuwa na Amurka Kroenke ya kasance wanda yafi kowa hannun jari a kulob din bayan daya sayi kason Danny Fiszman dana Lady Nina Bracewell-Smith akan fan miliyan 234.

Hamshakin dan kasuwa a Rasha Usmanov ya sayi hannun jari a Arsenal a shekara ta 2007.