Cole ya amince da tuhumar da FA tayi mashi

cole Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlton Cole

Dan kwallon West Ham Carlton Cole ya amince da tuhumar da hukumar kwallon Ingila FA ke mashi na aikata laifi akan kalaman da ya rubuta a shafin sadarwa na Twitter.

A lokacin wasan da Ingila ta shi kunen doki tsakaninta da Ghana a filin Wembley, Cole ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar"Jami'an hukumar shigi da fice sun ke waye filin Wembley!Na son tarko ne aka hada".

Daga baya Cole ya janye kalaman amma duk da haka sai da FA ta tuhumeshi.

Dan kwallon Ingilan wanda ya shafe shekara guda bai buga mata ba, a ranar Alhamis ya amsa laifin kuma da alamu za'a ci tararshi ko kuma a gargadeshi.

Cole wanda ya zira kwallo a West Ham sau goma sha daya a kakar wasa ta bana,ya amince ya bada ba'asi gaban kwamiti a ranar 21 ga wannan watan.

Ba a tunanin za a dakatar da dan kwallon mai shekaru 27 akan laifin.