FIFA ta nada Pele da Beckenbauer a kwamiti

brazil
Image caption Brazil tayi nisa a shirinta na 2014

An baiwa Pele matsayin mataimakin Franz Beckenbauer a kwamitin da FIFA ta nada don bada shawarwari akan hanyoyin inganta kwallon kafa kafin gasar cin kofin duniya da za ayi a Brazil a shekara ta 2014.

A ranar Alhamis ne FIFA ta sanarda kwamitin aiki da cikawa na mutane 22, wanda ya hada da Bobby Charlton, da Cafu da kuma Christian Karembeu.

Sauran kuwa sune tsaffin 'yan kwallon AC Milan wato Demetrio Albertini da Dejan Savicevic da Fernando Hierro da kuma dan Zambia Kalusha Bwalya.

FIFA ta kuma nada alkalin wasa Massimo Busacca da wasu jami'an kasashen da basu samu damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarun 2018 da 2022.

FIFA tace kwamitin zai yi zaman farko a ranar 10 ga watan Mayu a Zurich.