Carlos Tevez zai yi jinya ta makwanni hudu

tevez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carlos Tevez

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya tabbatar da cewa dan wasanshi Carlos Tevez ba zai buga wasansu na ranar Asabar ba tsakaninsu da Manchester United na kofin FA.

Dan kwallon Argentina din ya jimu ne a kafadarshi a ranar Litinin lokacin wasan da Liverpool ta casa City daci uku da nema.

A cewar Mancini"Tevez zai shafe makwanni uku zuwa hudu yana jinya".

Rashin Tevez babbar matsala ce ga City a kokarinta na lashe kofi a karon farko cikin shekaru 35, da kuma burin shiga sawun kulob hudu na farko a gasar premier ta Ingila.

Dan wasan mai shekaru 27 ya zira kwallaye 22 a wasannin daya bugawa City a kakar wasa ta bana, abinda yasa ake gannin shine dan kwallo mafi mahimmanci a kungiyar.