Akwai yiwuwar Chelsea ta sallami Ancelotti

Image caption Kocin Chelsea, Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea manager Carlo Ancelotti ya ce ba zai damu ba idan Chelsea ta sallame shi a karshe kakar wasan bana.

Kocin ne dai ya jagoranci Chelsea a bara, inda ta lashe gasar Premier da kuma gasar cin kofin FA.

A bana dai akwai yiwuwar kungiyar ba za ta lashe kofi, ko guda ba.

"Ba san makoma ta ba," In ji shi, Ya ce. "A karshen kakar wasan bana, kungiyar za ta yanke shawarar ko zan ci gaba da aiki da su. ko kuma a'a.

"Idan bashi ji dadin aiki na ba, za su iya sallama ta, domin ba zai dame ni ba." In ji Ancelotti.