Man City ba abokiyar hammayar mu bace- Scholes

Image caption Paul Scholes

Dadadde kuma gogaggen dan wasan Manchester United Paul Scholes ya ce kungiyar Man City ba abokiyar hammayar United ba ce.

Kungiyoyin biyu dai za su fafata ne a wasan kusa dana karshe a gasar cin kofin FA.

Manchester City, dai na da rabo ne kawai a gasar cin kofin FA, saboda ratar da aka bata a gasar Premier a yayinda United ke da rabo a gasar zakarun Turai da gasar Premier da kuma gasar cin kofin FA.

"Man City suna matsayin na hudu ko na biyar, saboda haka ko kusa damu basuyi ba. Ina ganin basa cikin rukunin wadanda zamu iya kira abokan hammayar mu." In ji Scholes.

"Manyan abokan hammayarmu sune su Arsenal da kuma Chelsea. Ina ganin mutane na ambato City ne saboda muna gari daya."