Kofin FA:City ta fidda United,Ferdinand ya soki Balotelli

magoya
Image caption Magoya bayan Man City da Man United

Dan kwallon Manchester United Rio Ferdinand ya nemi afuwa bayan rashin jituwar daya auku tsakaninshi da Mario Balotelli na Manchester City bayan wasansu na zagayen kusada karshe na kofin FA a Wembley.

Nasarar ta sanya City ta fidda United a yayinda Manchester City din zata jira wasan karshe na kofin FA.

Ferdinand yace"idan aka tashi wasa kamata yayi mutum ya tafi wajen magoya bayansu yayi murna bawai ya je wajen 'yan hammaya ba, ai wannan izgili ne".

City ta samu nasara ne ta wajen kwallon da Yaya Toure ya zira inda zata buga wasan karshe a ranar 14 ga watan Mayu.

Burin United na lashe kofina uku a kakar wasa ta bana ya ci karo da matsala, inda a yanzu abinda ya ragewa United shine gasar zakarun Turai dana kofin premier.