Elclassico:Real da Barca sun tashi kunen doki

messi
Image caption Ronaldo da Messi

Barcelona ta cigaba da baiwa Real Madrid tazarar maki takwas akan teburin La Liga bayan da manyan abokan hammayar suka tashi kunen doki a karawar da suka yi a karshen mako.

Wannan ne wasan farko da suka buga cikin guda hudu da zasu a cikin makwanni biyu.

Lionel Messi ne ya baiwa Barca nasara a bugun fenariti bayan Raul Albiol ta fadar da David Villa abinda ya sanya aka kori Albiol din daga wasan.

Real ta farke kwallonta ne bayan Daniel Alves ya kayarda Marcelo inda Cristiano Ronaldo yaci fenariti din.

Kungiyoyin biyu zasu kara a wasan karshe na kofin Copa del Rey a ranar 20 ga watan Afrilu sannan sai su hadu a zagayen kusada karshe na gasar zakarun Turai.

Sakamakon wasu daga cikin karawar na La Liga:

*Getafe 1 - 0 Sevilla *Málaga 3 - 0 Mallorca *Almería 0 - 3 Valencia