Dan kwallon Najeriya Adefemi ya mutu a Girka

Olubayo Adefemi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Olubayo Adefemi

Dan kwallon Najeriya Olubayo Adefemi ya mutu sakamakon hadarin mota, kamar yadda 'yan sanda a kasar Girka suka sanar.

Dan shekaru ashirin da biyar wanda ke takawa kungiyar Skoda Xanthi leda ya fadi ne a motarshi akan babban titin Egnatia.

Adefemi na tafiya akan hanyarsa daga Xanthi zuwa Salonika a yankin Kavala dake arewacin Girka.

'Yan sanda sun ce tsohon dan kwallon Rapid Bucharest yana kan hanyarsa ne don kamalla batun aurenshi lokacin da hadarin ya auku.

Adefemi ya kulla yarjejeniya da Xanthi a kakar wasan data wuce inda ya taka leda a wasanni 24 ya kuma zira kwallaye biyu.

Ya bugawa Najeriya kwallo a wasanni uku.