AYC:Najeriya ta lallasa Ghana daci biyu da daya

ayc
Image caption Najeriya ta taka rawar gani akan Ghana

Mai rike da kofin gasar kwallon matasan Afrika 'yan kasada shekaru ashirin da daya wato Ghana ta fara da kafar hagu bayan ta sha kashi a wajen Najeriya daci biyu da daya.

Innocent Uche Nwafor ne ya zira kwallayen biyu a wasan da Flying Eagles din ta samu galaba akan Black Satellites.

Wannan ce nasara ta farko da Najeriya ta samu akan Ghana a gasar matasa, saboda a baya Black Satellites dinne suka samu galaba a fafata uku na baya.

Ghana ta doke Najeriya daci daya da nema a shekarar 1993 sai kuma a shekara ta 2001 Ghana ta casa Najeriya daci hudu da daya sai kuma wasan karshe a 1999 inda Black Satellites din ta doke Flying Eagles.

Najeriya na fatar doke Kamaru a wasanta na gaba a ranar Alhamis don hagen tsallakewa zuwa zagayen kusada karshe.

Ghana zata iya farfado da kokarinta na tsallakewa zuwa zagaye na gaba inda har ta samu galaba akan Gambia a ranar Alhamis.

Kasashe hudun da suka tsallake zuwa zagayen kusada karshe zasu wakilci Afrika a gasar cin kofin duniya a Columbia a watan Yuli.