An zabi Gareth Bale zakaran dan kwallon Premier

Jack Wilshere
Image caption Jack Wilshere aka zaba matashin da ya fi kowanne

Kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa na Premier a Ingila sun zabi dan wasan Tottenham Gareth Bale a matsayin zakaran gasar Premier na bana.

Dan wasan mai shekaru 21, ya zira kwallaye 11 a wasanni 36 a kakar bana, shi ne dan wasa na hudu daga kasar Wales da ya lashe kyautar, bayan Ian Rush da Mark Hughes da Ryan Giggs.

Ya ce: "Abu ne na alfahari idan kaga sunanka a cikin jerin sunayen wadanda suka taba lashe gasar."

Haka kuma an zabi dan wasan Arsenal Jack Wilshere, mai shekaru 19, a matsayin matashin da ya fi kowanne taka leda a gasar ta Premier a bana.

Gareth Bale ya doke Charlie Adam da Samir Nasri da Scott Parker da Carlos Tevez da Rafael van der Vaart da kuma Nemanja Vidic, wajen lashe wannan kyauta.