Cameroon ya nemi a yi shagulgula

Cameroon ya nemi a yi shagulgula Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan biki na da mahimmanci ga jama'ar Burtaniya

Fira Ministan Burtaniya David Cameroon ya yi kira ga 'yan kasar da su fita domin yin shagulgula domin nuna farin ciki da bikin gidan sarautar Burtaniya.

David Cameroon ya kuma nemi shugabannin kanan Hukumomi da kada su sa baki a shagulgulan, bayan da aka samu rahotannin kafa wasu ka'idoji.

Ya ce ranar 29 ga watan Afrilu "dama ce... a gare mu ta yin murna kan wani muhimmin abu kan kasarmu".

Wannan bayanin na zuwa ne bayan da bayanai suka nuna cewa an samu bukatar neman izini 4,000 domin gudanar da shagulgula na kan titi a lokacin bikin a Ingila da Wales.

A kalla mutane miliyan biyu ne za su shiga shagulgulan da za a yi a kan tituna domin murnar bikin Yarima William da Kate Middleton.

Mr Cameroon zai ziyarci Arewacin Ingila tare da matarsa, Samantha, domin tallata shagulgulan.

'Babbar dama'

Sashin kula da jama'a da kuma kananan hukumomi ya bada umarni ga kananan hukumomin da suke kokarin hana shagulgulan bikin ba tare da wani sharadi ba.

Sakataren kula da kananan hukumomi Eric Pickles ya ce "Wannan dama ce da za ta baiwa mazauna yankuna daban daban damar haduwa wuri guda".

"Duk da cewa mutane za su so kasancewa cikin lafiya, amma suna da damar kalubalantar matakan da hukumomi ka iya dauka na danne mu su hakkinsu".