Sahin ba zai kara taka leda a kakar bana ba

Nuri Sahin
Image caption Nuri Sahin ya taka rawa sosai a Dortmund a kakar bana

Dan wasan Borussia Dortmund Nuri Sahin, ba zai kara taka leda a kakar bana ba, sakamakon raunin da ya ke fama da shi.

Dan wasan mai shekaru 22 ya samu raunin ne a wasan da kungiyar shi ta lashe Freiburg da ci 3-0, inda ya fita daga wasan bayan minti 28 da farawa.

Tiyatar da aka yi masa a ranar Litinin, ta nuna cewa abin ya yi muni, inda rahotanni suka nuna cewa ba zai kara taka leda a bana ba. Likitan kungiyar ya tabbatar da cewa dan wasan zai shafe akalla makwanni shida yana jinya.

"Zai yi wuya Nuri ya kara taka leda a kakar bana," kamar yadda ya shaida wa Kicker.de.

Kwallaye shida da Sahin ya zira a wasa 30 sun taimakawa Dortmund ci gaba da mamaye gasar Bundesliga.

A yanzu dai sun baiwa Bayer Leverkusen tazarar maki takwas, kuma suna kan hanyar lashe gasar a karon farko cikin shekaru tara.