'Yan kwallon Chelsea Alex da Ramires za suyi jinya

Alex da Remires Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alex da Remires

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti yace 'yan kwallonshi Alex da Ramires zasu jinya sakamakon rauni a kafadarsu.

'Yan kwallon biyu ba zasu buga wasan Chelsea da Birmingham da kuma West Ham.

Amma dai Ancelotti ya hakikance Fernando Torres zai bada mamaki kafin karshen kakar wasa ta bana.

An siyo Torres akan pan miliyan hamsin daga Liverpool a watan Junairu.

Haka zalika Ancelotti yaki tabbatar da cewa ko za a fara wasan Chelsea da Birmingham ranar Laraba ko kuma a a.