Tottenham a canza lokacin wasan City da Stoke

redknapp
Image caption Harry Redknapp

Tottenham na son a matsar da wasan Manchester City tsakaninta da Stoke na gasar premier gaba.

Za ayi wasan ne a ranar 14 ga watan Mayu, amma saboda kungiyoyin biyu zasu kara da juna a wannan ranar a wasan karshe na kofin FA, sai aka dage wasan premier din nasu zuwa 17 ga watan Mayu.

Idan Stoke ta samu nasara ko aka tashi canjaras,sakamakon zai taimakawa Spurs a kokarinta na shiga gaban Manchester City don samun gurbin zuwa gasar zakarun Turai.

Amma Stoke din zata iya tsallakewa zuwa gasar Europa idan har Manchester City ta karke cikin kulob hudu na farko a premier.

Kocin Tottenham Harry Redknapp yace "ya kamata mahukunta su duba, don muna son a canza".

Manchester City a yanzu itace ta hudu akan tebur, a yayinda Spurs take ta biyar amma tana da kwanta wasa.

Tottenham nada sauran wasanni bakwai a gasar premier a kakar wasa ta bana, a yayinda da zata kara da Arsenal a ranar Laraba.

Har wa yau Tottenham na da wasanni a nan gaba tsakaninta da Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool.