Manchester United ta nemi afuwa akan batun Wembley

united
Image caption Manchester United

Manchester United ta nemi afuwa kuma tace zata biya abubuwa da suka lalace a Wembley bayan wasanta na gasar cin kofin FA.

United ta ce ta janyo hankalin hukumar kwallon Ingila akan lalata abubuwa bayan kashin data sha akan Manchester City daci daya me ban haushi.

Hukumar FA ta ce ba zata hukunta United ba akan lamarin.

A lokacin wasan United da City din dai an baiwa Paul Scholes jan kati saboda irin tokarin daya kaiwa Pablo Zabaleta.

Har wa yau, bayan an tashi wasan 'yan kwallon United Rio Ferdinand da Anderson sun yi fito na fito dan kwallon City Mario Balotelli.