Blatter ya ce zai samarda fan biliyon daya

blatter Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter da Bin Hammam

Sepp Blatter ya fitar da manufarshi na batun sake zabenshi a matsayin shugaban Fifa inda ya bada fifiko akan bukatar samun lumana da tabbatacciyar cigaba a hukumar.

A wasikar daya aikewa duka wakilan Fifa na kasashe 208, Blatter ya dauki alkawarin samarda fan biliyon daya cikin shekaru hudu don ayyukan bunkasa kwallon kafa.

Dan kasar Switzerland mai shekaru saba'in da biyar, yana kokarin samun wa'adi na hudu a ofis, inda Mohammed bin Hammam shugaban hukumar kwallon Asiya ke kalubalantarshi a zaben da za ayi a ranar daya ga watan Yuni.

Blatter yace"Fifa ce rayuwata, kwallo ne rayuwa ta.Ina da gogewa da dabarun ciyyar da hukumar gaba".

Wasikar Blatter na zuwa ne wata guda bayan da Bin Hammam ya sha alwashin rarraba karfin Fifa a tsakanin nahiyoyi shida, sannan kuma ya samarda karin kujeru 17 a kwamitin gudanarwar Fifa.

Bugu da kari Bin Hammam din ya ce zai rubanya yawan kudaden da Fifa ke baiwa kasashe.