Caf ta ci tarar Zamalek fan dubu tamanin

caf
Image caption Zamalek ta saba ka'idar CAF

Hukumar kwallon Afrika Caf taci tarar kungiyar Zamalek fan dubu tamanin sannan an umurceta da buga kwallo ba tare da 'yan kallo ba.

Wannan hukuncin ya biyo bayan tashin hankalin daya barke lokacin wasan Zamalek da Club Africain ta Tunisia a birnin Alkahira.

Caf a ranar Laraba ta kama Zamalek da laifin saba dokarta na da'a saboda magoya bayanta sun kaiwa 'yan kwallo da alkalan wasa hari.

Caf ta yanke hukuncin cewar Zamalek zata buga wasanninta hudu masu zuwa ba tare da 'yan kallo ba.

Zamalek na daga cikin hukunce hukunce goma da Caf ta dauka a taron ta na Johannesburg, inda kuma aka ci tarar Senegal dala dubu biyar saboda magoya bayanta sun shigo fili a wasan share fage tsakaninsu da Kamaru.