Arsenal bata da dabi'ar nasara-Fabregas

fabregas
Image caption Cesc Fabregas

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas ya ce kungiyar bata da dabi'ar samun nasara, itace tasa tun shekara ta 2005 babu bata lashe kofi ba.

Dan kwallon mai shekaru 23 ya ce kocinsa Arsene Wenger da a Spain da an koreshi.

Yace"a tunani na babu dabi'a ta nasara, babu gogewa a wannan lokacin, amma muna da zaratan 'yan kwallo sai dai ba suda kwarin zuciya"

Gunners din zata kara da Tottengham a ranar Laraba, a wasan da zai nuna ko zata iya lashe gasar premier ko kuma a a.

Kuma duk sakamakon da ba nasara bace ga Arsenal tabbas kenan zata shafe shekaru shida babu kofi.

Fabregas ya koma Arsenal ne daga Barcelona a shekara ta 2003.

An yi cece-kuce akan makomarshi a shekara ta 2010 akan cewar ze koma Barcelona akan fan miliyan talatin, amma sai yaki amincewa.

Kwangilar Fabregas a Emirates zata karke ne a shekara ta 2014.