An tashi canjaras tsakanin United da Newcastle

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sir Alex Ferguson bai ji dadin yadda wasan ya kasance ba

Manchester United ta barars da damar da ta samu ta kara tazarar da ke tsakaninta da Arsenal a saman gasar teburin Premier, bayan da suka tashi canjaras da Newcastle.

United ba su yi wasa kamar yadda ya kamata ba dai, duk da cewa Wayne Rooney da Ryan Giggs sun zubar da damarmaki.

Javier Hernandez ya yi korafin samun fanareti, amma a karshe ya buge ne da samun katin gargadi daga alkalin wasan.

Newcastle sun cancanci samun maki dayan da suka samu, kuma su ma sun yi korafin cewa sun samu fanareti.

Sakamakon wasan dai na da mahimmanci ga Newcastle, domin zai taimaka musu a kokarin da suke yi na samun tabbacin zama a gasar Premier.