Na ji takaicin ihun da aka yi mini a Newcastle-Owen

owen
Image caption Micheal Owen

Dan kwallon Manchester United Micheal Owen ya ce yaji takaicin ihun da magoya bayan Newcastle suka yi mashi a lokacin wasan da suka tashi babu ci a St James Park.

An yiwa tsohon dan kwallon Newcastle ihu lokacin da aka sakoshi a minti na tamanin da daya.

Owen a shafinsa na Twitter"An yi mani mumunar tarba kuma abin takaici ne, naso in zira kwallo".

Owen ya koma Newcastle daga Real Madrid akan fan miliyan 16 a shekara ta 2005 inda ya zira kwallaye 30cikin karawa 79 daya buga a St James Park.

Tarihin kwallon Owen: * Manchester United: Wassanni 44 kwallaye 13 * Newcastle United: Wassanni 79 kwallaye 30 * Real Madrid: Wassanni 40 kwallaye 14 * Liverpool: Wassanni 297 kwallaye 158 * England: Wassanni 89 kwallaye 40