Platini ya nemi afuwa akan farashin tikiti

platini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Michel Platini

Shugaban Uefa Michel Platini ya nemi afuwa akan tsawallalen farashi tikitin shiga kallon wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a filin Wembley a wata mai zuwa.

A cewar Uefa din a nan gaba zata bullo da farashi mai sauki ga iyalai don kallon wasan karshen.

An yita sukar farashin tikitin da aka sanar inda mafi karanci yake akan fan 176.

Platini wanda yake London don mikawa magajin garin London Boris Johnson kofin gasar, yace bisa kuskure ne aka tsara farashin tikitin.

Wasan karshen ya dawo London a karo na shida kuma a karon farko a Wembley tun bayan da aka yi mashi kwaskwarima.

Cikin kungiyoyi hudu daya ne zata lashe kofin wato a tsakanin Manchester United ko Schalke 04 ko Barcelona ko kuma Real Madrid.