Muna da damar lashe Premier - Ancelotti

Carlo Ancelotti Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Carlo Ancelotti yana fuskantar kalubale a bana

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya umarci 'yan wasansa da su lashe wasanni biyar din da suka rage musu domin tankado Manchester United daga saman teburin gasar Premier.

"Maki shida ne tsakaninmu kuma abu ne mai wahala mu ka mo su," a cewar Ancelotti, wanda kungiyarshi ta lashe Birmingham da ci 3-1 ranar Laraba.

"Burinmu shi ne mu lashe dukkan wasannin da suka rage. Abu ne mai wahala amma shi ne burinmu.

"Muna da kwarin gwiwa har zuwa ranar karshe."

Florent Malouda ne ya zira kwallaye biyu a wasan na Birmingham, inda ya zira kwallon farko jim kadan da fara wasan.

Arsenal ta tashi 3-3 tsakaninta da Tottenham, abinda ya baiwa Chelsea damar darewa mataki na biyu, sai dai yawan kwallaye ne ya raba tsakaninsu da Arsenal.