An kwantar da Gerard Houllier a asibiti.

houllier Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gerrard Houllier

An kwantar da kocin Aston Villa Gerard Houllier a asibiti.

Dan shekaru sittin ukun a daren jiya ne aka kaishi asibiti a Birmingham, kamar yadda kungiyar ta sanar.

Tuni yayi magana da shugaban kungiyar Paul Faulkner inda yace rashin lafiyar ba mai tsanani bane.

Mataimakinshi Gary McAllister shine ya lura da horon 'yan wasan da aka yi a ranar Alhamis.

Houllier ya yiwa magoya bayan kungiyar godiya saboda nuna damuwarsu akanshi.

Ana saran zai cigaba da kasancewa a asibiti na kwanaki inda za a dinga mashi gwaje-gwaje.

McAllister ne zai jagoranci Aston Villa a wasanta na gasar premier da Stoke City a ranar Asabar.