Arsenal ba zata iya lashe gasar Premier ba- In ji Redknapp

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kocin Tottenham, Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp yayi imanin cewa Arsenal ba baza iya lashe gasar Premier ta bana ba.

Kocin ya ce yana da kwarin gwiwa cewa Manchester United ce za ta lashe gasar ta bana.

Har wa yau, Redknapp ya ce Chelsea ma tana da hurumin lashe gasar, amma ba'a maci tuwo ba, sai miya ta kare.

"A gaskiya bani da kwarin gwiwa akan Arsenal, amma ina ganin Manchester United za ta iya lashe gasar, kuma tana iya kaiwa ranar karshe." In ji Redknapp