Stephane Mbia ya samu rauni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stephane Mbia

Kokarin kungiyar Marseille na lashe gasar Faransa na gamu da cikas bayan dan wasan ta Stephane Mbia ya samu rauni.

Dan wasan wanda dan asali Kamaru ne ba zai taka leda ba na tsawon makwanni uku.

A yanzu haka dai kocin kungiyar Didier Deschamps na fuskantar kalubalen rashin manyan 'yan wasan sa a yayinda kakar wasan ke kawo karshe.

An dai fidda dan wasan ne bayan minti bakwai a wasan da kungiyar ta doke Montpellier a ranar asabar.

Likitoci sun ce Mbia ba zai samu taka leda ba a wasannin bakwai din da suka rage a kakar wasan bana.

"Gaskiya bamu ji dadin labarin ba". In ji Kocin Marseille, Didier Deschamps.