Nadal ya lashe gasar Barcelona Open

Image caption Rafeal Nadal

Shahararren dan wasan Tennis din nan wanda shine na daya a duniya Rafeal Nadal ya lashe gasar Barcelona Open a karo na shida.

Rafael Nadal ya yi galaba ne a kan David Ferrer da maki 6-2 6-4 a wasan karshe da suka fafata.

A yanzu haka dai ba'a doke Nadal mai shekaru 24 da haihuwa ba a wasan kan laka sau 34, kuma akwai yiwuwar zai lashe gasar French Open da za'a yi a watan Yuni.

Nadal ya lashe gasar Barcelona Open a shekaru biyar kenan a jere inda ya doke Ferrer a wasan karshe a shekarar 2008 da kuma 2009.

Dan wasan dai bai halarci gasar ba a shekarar 2010 saboda raunin da ya samu a gwiwarsa.