Alkalan wasa ne ke taimakawa Barca - Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho ya yi korafi kan yadda aka kori Pepe daga wasan

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce alkalan wasa ne suke taimakawa Barcelona, kuma bai san dalilin da ya sa suke yin hakan ba.

Mourinho yana maida martani ne bayan da Barcelona ta doke Madrid da ci 2-0 a zagayen farko na wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Ya ce: "A zahiri take cewa idan kana karawa da Barcelona to baka da wata dama.

"Ban sani ba ko tallan da suke yiwa Majalisar Dinkin Duniya ne yasa, ko kuma saboda suna da kyau ne, amma dai suna da wannan ikon."

Mourinho ya kara da cewa: "Ban sani ba ko don alakar da ke tsakanin shugaban Hukumar Kwallon Spain ne - wanda shi ne mataimakin shugaban Hukumar kwallon Turai ta Uefa".

Mourinho yana korafi ne kan jan katin da aka baiwa Pepe bayan ya tade Dani Alves a lokacin ana 0-0 a wasan.

Shi ma kansa Mourinho an kore shi daga filin inda ya koma kallo daga sama, bayan da ya koka kan katin da aka baiwa Pepe.

Guardiola kwararran koci ne, amma ya dauki kofin zakarun Turai, wanda abin kunya ne a wuri na ace na dauka sakamakon rudanin da ya faru a Stamford Bridge, haka kuma bana idan ya kara dauka, to zai zamo ne bayan rudanin da ya faru a Bernabeu," a cewar Mourinho.