Olympic: An nemi tikiti sama da miliyan 20

Hakkin mallakar hoto other

Masu shirya gasar Olympic da za'a yi a Landan a shekarar 2012 sun ce an nemi tikiti kallon gasar wanda ya kai sama da miliyan 20.

Kwamitin shirya gasar ya ce wajen mutane miliyan daya da dubu dari takwas ne suka nemi tikitin kallon gasar. Adadin tikitin da aka nema ya ninka tikiti miliyan shida da dubu dari shida da aka samarwa 'yan kallo a Burtaniya domin ganin gasar.