AYC: Najeriya ta kai wasan karshe

Najeriya ta kai wasan karshe a gasar cin kwallon Afrika ta matasa da kasar Afrika ta kudu ke daukar bakonci.

Najeriyar dai ta doke Mali ne a wasan kusa dana karshe da ci biyu da nema.

Dan wasan Najeriya Innocent Nwofor Uche, ne ya zura kwallon farko a wasan, wanda kuma harwa yau itace kwallonsa ta uku a gasar.

Sannan kuma ana karin lokaci Stanley Okoro ya zura ta biyu ana bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Najeriya na neman lashe gasar ne a karo na shida , kuma za ta kara da Kamaru ko Masar ne a wasan karshe a ranar lahadi.