An dakatar da jami'in FFF akan wariyar launin fata

French Football Federation' Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana batun wariyar launin fata a Faransa

Hukumar dake kula da kwallon Faransa-FFF ta dakatar da darekta wasanni Francois Blaquart daga mukaminshi.

Dakatarwar nada nasara ba batun kayyade yawan bakin da za a dauka su takawa kasar kwallo.

Rahotanni sun nuna cewar, manyan jami'an FFF sun amince a asirce wajen kayyade yawan bakaken fata da larabawa da zasu buga kwallo 'yan shekaru 12 zuwa 13 kada su wuce kashi talatin cikin dari.

Blaquart da kocin Faransa Laurent Blanc sunce an kururuta kalaman.

Ana binciken zargin kuma ana saran bayan kwanaki takwas za a kamalla binciken.

Ministan wasannin Faransa Chantal Jouanno da shugaban FFF Fernand Duchaussoy sune suka dakatar da Blaquart.