Chelsea na da damar lashe Premier- Ferguson

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya soki alkalin wasa Chris Foy bayan da kungiyarshi ta sha kashi a hanun Arsenal da ci daya mai ban haushi. Duk da dai kocin ya yarda cewa an hanawa Arsenal fenarity, Ferguson ya soki kocin da hanawa United Fenarity bayan da aka tade Micheal Owen a lokacin da aka kusan kammala wasan.

"Wannan ya ba Chelsea damar lashe gasar Premier- kuma ina ganin matakin da alkalin wasan ya dauka ne ya haddasa hakan." In ji Ferguson.

Chelsea na bayan United ne wanda ke jan ragama a gasar ta Premier da maki uku, kuma kungiyoyin biyu za su kece raini ne a Old Trafford a ranar lahadi.

"Wannan babban wasa ne, kuma ya kamata ace alkalan wasa suna daukan matakan da suka dace." In ji Ferguson.