Wilshere na son bugawa matasan Ingila - Pearce

Wilshere Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jack Wilshere yana taka leda sosai a Arsenal

Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya bayyana aniyarsa ta bugawa Ingila kwallo a gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekaru 21 na Turai, kamar yadda Stuart Pearce ya bayyana.

Shi dai kocin Arsenal Arsene Wenger ya yi Allah wadai da gayatar da aka yi ma Wilshere dan shekaru 19, wanda yanzu yake takawa babbar tawagar Ingila leda.

Sai dai kocin tawagar ta Ingila Stuart Pearce, ya bayyana cewa Jack ya nuna sha'awarsa ta taka leda a gasar.

"Aikin kulob shi ne ya sa ido kan abin da 'yan wasa suka nuna sha'awar yi, idan suna so su halarci gasar to dole sai dai a samu musu ido", a cewar Pearce.