Fifa ba zata shiga cikin matsalar GFA ba

fifa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shakwatar FIFA

Fifa ta ce bata da hurumin shiga tsakani akan takaddamar shugabancin a hukumar kwallon Ghana wato GFA.

'Yan takarar shugabanci biyu sun rubuta takardar koke zuwa Fifa akan hanasu shiga takara da akayi.

Kwamitin lura da zaben GFA ta hana Neil Armstrong Mortagbe da Vincent Sowah Odotei shiga takara akan cewar akwai wasu matsaloli a wajen cike takadar nuna sha'awar takara.

Fifa ta bukaci mutanen biyu su warware matsalar a gida don ba zata shiga cikin batun ba.

Mataimakin shugaban Fifa Markus Kattner yace"wannan batun ya shafi GFA ne kadai, ba zamu shiga ciki ba".

Hana mutanen biyu takara, yasa shugaba mai ci a yanzu Kwesi Nyantakyi a matsayin wanda yayi takara shi kadai a zaben da za a gudanar a nan gaba.