Fifa ta sake nazari akan amfani da na'urar fasaha

blatter
Image caption Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta fidda jadawali akan yiwuwar amfani da fasahar zamani wajen tantance shigar kwallo a raga.

A wannan shekarar ne Fifa zata karbi rahoton karshe daga wajen kungiyar kwallon na kasa da kasa.

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya bayyana cewar watakila ayi amfani da na'urar fasaha a lokacin gasar cin kofin duniya da za ayi a shekara ta 2014 a Brazil.

Fifa ta gayyaci kamfanonin dake da sha'awar samar da na'urar fasahar daga nan zuwa ranar uku ga watan Yuni don a gwadasu daga watan Satumba zuwa Disamba.

A sake maidoda mahawara akan batun amfani da fasaha saboda a ranar Asabar lokacin wasan Chelsea da Tottenham kwallon karshe da aka ci, ya nuna cewar bai karasa shiga raga ba.