Muntari ya yi mana tsada-Sunderland

Sulley Muntari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sulley Muntari

Wakilin dan kwallon Ghana Sulley Muntari ya bayyana cewar Sunderland ba zata iya sayen dan wasan ba na dun dun dun saboda albashinshi yayi yawa.

Tun a watan Junairu ne, Muntari ya bar Inter Milan ya koma Sunderland a matsayin aro.

A cewar wakilin wato Fabien Piveteau, babu yiwuwar kulla yarjejeniya da Sulley a Sunderland saboda sunce yayi tsada.

Amma dai yace John Mensah zai cigaba da taka leda a Black Cats.

Piveteau ya kara da cewar Sulley wasanni goma sha takwas kadai zai bugawa Sunderland.

Sai dai a halin da ake ciki a yanzu Muntari bai ci kwallo ko guda ba cikin wasanni takwas a Black Cats.