United ta kara farashin tikitin shiga Old Trafford

Filin wasa na Old Trafford
Image caption Filin wasa na Old Trafford na daukar fiye da mutane sittin

Manchester United ta kara kudin tikitin shiga kallon wasa a filinta na Old Trafford da fan guda a kan kowanne wasa daya daga kakar wasanni mai zuwa.

Kulob din ya ce ya dauki matakin ne sakamakon kudin harajin da aka kara a kasar Ingila.

Kulob din ya kuma amince ya rage farashin tiketin da magoya bayansa 'yan shekara 16 zuwa 17 suke biya.

Wannan matakin dai ya zo ne kwana guda bayan da Arsenal ta kara farashin na ta kudin tikitin da kashi 6 da rabi cikin dari, matakin da kungiyar magoya bayanta suka soka.

Wannan dai na nufin magoya bayan United din da ke son sayen babban tikiti za su biya fan 950 domin kallon wasanni 19 na gasar Premier a filin wasa na Old Trafford.